
Da Dumi Duminsa! Sojoji sun tabbatar da juyin mulki a kasar Benin.
Sojoji a Jamhuriyar Benin sun sanar da yin juyin mulki a ranar Lahadi, inda suka tsige Shugaba Patrice Talon.
Sojojin sun sanar da Laftanal Kanal Tigri Pascal a matsayin sabon shugaban soji a ƙasar.
France24 ta ruwaito, sojoji ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanar Pascal Tigri sun karɓe iko da tashar talabijin ta ƙasa, suka kuma bayyana cewa sun “hambarar da Talon daga mulki.”