1758915406320.Screenshot 20250926 203553

An samu gawarwakin yara uku a cikin motar mahaifinsu a Borno

An gano gawarwakin yara uku a cikin motar mahaifinsu a unguwar Zannari da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Mahaifin guda biyu daga cikin yaran, Babagana Zanna Jaridama, sanannen mai sukar lamurran siyasa a kafafen sada zumunta, ya yi zargin cewa kashe yaran aka yi don ya wallafa wani rubutu kwanan nan, inda ya zargi wasu ‘yan siyada da yi wa Gwamna Babagana Zulum zagon ƙasa.

Da ya ke magana da jaridar Daily Trust, Zanna ya ce wata mata da ba a san ko wacece ba ta yi awon gaba da yaran a ranar Talata, kafin daga baya a jefa gawarwakin a cikin motarsa.

“A ranar Talata, ɗan makwabcinmu da ke wasa da su ya ruga ya sanar da iyalina cewa wata mata ta kira yaran da sunan za ta ba su sadaka, amma maimakon haka ta yi awon gaba da su.

“Yara biyu daga cikinsu ‘ya’yana ne, yayin da na uku ɗan makwabcinmu ne. Anwar, mai shekara uku, ɗan suna ne da Gwamna Zulum, yayin da Fatima, wacce aka fi sani da Mama, tana da shekara biyu kacal,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa bayan kwana biyu na neman-gaggawa da kuma roƙon a sako su, sai aka gano gawarwakin yaran a cikin motarsa da misalin tsakar dare a ranar Alhamis.

Zanna ya tabbatar da cewa ya kai rahoton satar da kuma kisan ga ‘yansanda, inda ya bukaci a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da adalci.

Haka kuma ya bayyana cewa an kai gawarwakin yaran asibiti domin a gudanar da binciken likitanci (autopsy) don gano musabbabin mutuwar su.

Ƙoƙarin da aka yi na tuntubar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ci tura, domin bai ɗauki kiran waya ba kuma bai mayar da martani ga saƙonnin da aka tura masa ba.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version