GridArt 20250923 111901753

AN BUKACI MAWADATA DASU DUNGA TAIMAKAWA KUNYOYIN DA SUKE TALLAFAWA MARAYU – SAKIN KANO ALHAJI AMINU ADO BAYERO.

Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi wannan Kiran ne a lokacin da Gidauniyar Fadalu Rabbi Charity Foundation Suka ziyarceshi a Fadarsa.

Sarkin Yace aikin Kungiyar Wani bangare ne na taimakawa al’uma kamar yadda Addini yayi Umarnin Kan taimakawa Marayu.

Yayi adduar ga Allah ya taimakesu akan wannan aiki tareda basu ladan da Allah yayi alkawarin bawa wadanda sukayi wannan aiki.

Sarkin ya Tabbatar musu da dukkan Hadin kan masarautar Domin su cigaba da samun Nasarar abubuwan da suka sa a gaba.

Ya horesu dasu tsarkake zukatansu akan wannan aiki, kasancewar Allah Yana duban zukata ne akan dukkan Ayyuka, Kamar yadda Sarkin yace idan Allah ya dubi zukatansu to ko shakka Babu zai taimakesu akan ayyukan su.

Yace bisa ga dukkan da Kuma yadda shugaban Kungiyar ya Gabatar da jawabinsa ya Tabbatar da suna kyakkyawar niyya a zukatansu na aiwatar da wannan aiki.

Yayi musu nasiha akan su cigaba dayin dauriya da jajircewa da Kuma aiki tukuru da dukkan abunda Zasu iya yi Domin taimakawa Marayu da iyayen Marayu Mata.

Yaja hankalin Wadanda suke karbar taimakon dasu Sani cewa Wani taimako ne yazo daga Allah garesu, yace dukkan abubuwan da suka samu suyi amfani dashi ta hanyar data dace, Yana Mai cewar Zata iya kasancewa anan gaba suma Zasu iya taimakawa wasu kamar yadda suma aka taimakesu.

Tunda farko Shugaban Kungiyar Malam Abbas Ahmad yace sunje Fadar Sarkin ne sunzo fadar Sarkin ne Domin sanar dashi irin Ayyukan da Gidauniyar takeyi Wadanda suka hadar da Taimakawa Marayu da Mata iyayen Marayun.

Malam Abbas yace hatta Matasa Wadanda suke fadace fadacen Daba da Kuma shaye Shaye Kungiyar tasu tana kokarin ganin ta tallafesu Domin dawo da rayuwarsu Kan dai dai.

Yace Wadannan na daga cikin dalilai da suka sa tareda dacewar suzo Domin Gabatar da kansu ga Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero tareda dasa musu albarka a cikin ayyukan su.

Sa Hannu.

Abubakar Balarabe Kofar Naisa

Sakataren Yada labarai na

Mai Martaba Sarkin Kano

Alhaji Aminu Ado Bayero CFR JP CNOL

23/09/2025

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version