Daga Ikramatu Sulaiman:

GridArt 20250910 200834716

AN BUKACI MATASA SU CIGABA DABIN TURBAR YABON MANZON ALLAH (SAW) – SARKIN KANO BAYERO

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero shine yayi wannan Kiran lokacin da Gidauniyar Masoya Annabi Muhammadu SAW wadda akewa lakabi da “ANNABI NAMU FOUNDATION suka ziyarceshi a fadarsa dake Gidan Nassarawa a Birnin Kano.

Sarkin ya nuna farin cikinsa bisa ziyarar da suka Kai masa wadda Tayi dai dai da watan da aka haifi Annabi Muhammadu SAW.

A don haka hakane yayi kira ga sauran Matasa su cigaba da yabon Annabi tsira tareda girmamashi, inda yayi fatan Yan Kungiyar su cigaba da Jan hankalin sauran Matasa Domin su raja’a akan nuna kauna da soyayya ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu SAW da iyalan gidansa da Sahabbansa da Kuma sauran Mabiyansu.

Yayi fatan zasu kasance masu Da’a da biyayya ga Iyayensu da Malamansu tareda kira a garesu su cigaba da neman ilimi, inda ya Tabbatar musu da dukkan Hadin Kai da goyon bayan Masarautar ta Kano.

Tunda farko da yake Jawabi Shugaban Gidauniyar Malam Usama Bala Sani yace sunje Fadar Sarkin ne Domin nuna Mubaya’arsu ga Sarkin tareda neman Tubarriki da Kuma sawa Gidauniyar tasu Albarka.

Malam Usama ya tabbatarwa da Sarkin Hadin kansu da goyon bayansu Domin cimma duk wata Nasara da akasa a Gaba.

A wani cigaban Kuma Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi Kyautar Alqur’ani Mai Tsarki daga Makaman Dogaran Sarkin Ilori Malam Hussaini Dogari a Wata ziyara ta Muusamman da ya kawo masa har Jihar Kano Domin nuna soyayya da kauna a gareshi.

Sarkin ya gode masa tareda yi masa fatan alheri da Kuma komawa kasarsa lafiya.

Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version