IMG 20251007 094607

Akalla mutane hudu ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru da yammacin Lahadi a kan babban titin Kaduna–Abuja, kusa da Kakau, Gonin Gora, a jihar Kaduna.

‎Hukumar Kiyaye Hadura ta Ƙasa (FRSC), reshen jihar Kaduna, ta tabbatar da faruwar hatsarin. Kwamandan FRSC na jihar, Iliyasu Tijjani, ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, lokacin da motar Hilux mai saurin gaske ta yi karo da tankar gas.

‎Mutuwar Tsohon Sojan Nijeriya Ta Tilasta Jirgin British Airways Saukar Gaggawa A Barcelona

‎ “Binciken farko ya nuna cewa gudu fiye da ƙa’ida da gangancin wucewa sune manyan abubuwan da suka haddasa hatsarin,” in ji Tijjani.

‎A cewar FRSC, mutane biyar ne ke cikin motar Hilux – maza hudu da mace ɗaya. Duk maza hudu sun mutu a Asibitin St. Gerard Catholic, yayin da mace ɗaya ke samun kulawa a Asibitin FRSC, Tollgate, Kaduna.

‎Karon ya lalata motar Hilux sosai, sannan ya janyo cunkoson ababen hawa na ɗan lokaci kafin jami’an ceto su isa wurin.

‎Kwamandan ya yi kira ga direbobi da su guji gudu fiye da ƙa’ida da gangancin wucewa, yana mai jaddada cewa mafi yawan hatsarurrukan da ke faruwa a titin Kaduna–Abuja na faruwa ne saboda rashin haƙuri da take dokokin zirga-zirga.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version