Screenshot 20251005 153754 Google

2027: Ɓangaren Kudu-maso-Yamma na tare da Tinubu — APC

Jam’iyyar APC a Jihar Legas ta ce yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya ba zai yi watsi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba a zaben 2027.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Seye Oladejo, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Legas, yana mayar da martani ga magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Dr. Gbenga Olawepo-Hashim, da suka ce yankin ba zai sake zaɓar Tinubu ba.

Oladejo ya bayyana cewa Tinubu zai doke duk wani yunƙuri da ke neman hana shi nasarar sake takara, yana mai cewa Olawepo-Hashim ba shi da ƙaƙƙarfan tsari na siyasa kuma ba shi da ƙwarewar lashe zabe.

Ya kare gwamnatin Tinubu, yana cewa tana shimfiɗa ginshiƙan ci gaba a fannoni da dama kamar aikin raya kasa, ilimi, noma, tsaro da tattalin arziki.

Oladejo ya kuma zargi ‘yan adawa da yin amfani da bayanai na son rai da siyasa ta kafar labarai maimakon aiki, yana mai jaddada cewa “Yammacin Najeriya ba zai bar ɗansa ba saboda wani abu na siyasa marar ma’ana.”

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version