
Daga Abubakar DK:
Kwamitin Gawuna-Garo Strategic Project ƙarƙashin jagorancin Hon. Muhammad Badaru Umar Ungogo ya kai ziyara ta musamman da jaddada zumunci ga wanda yayi wa Jam’iyyar APC Takarar Ɗan Majalisar Dattawa na Kano Ta Tsakiya, Alh. Abdulsalam Abdulkarim (A.A Zaura), a ofishin sa dake Babban Birnin Tarayya Abuja.
Da yake jawabi Hon. Abdulsalam A.A Zauran ya bayyana matuƙar godiyar sa da murna da wannan babbar ziyara tare da tabbatar da jaddada mubaya’ar sa ɗari bisa ɗari ga wannan tafiya ta Gawuna-Garo, inda cikin maganar sa yake cewa a iya tunanin sa tunda duk nagarta da wata daraja da kuma gogewa kowacce iri ce da ake nema akwai ta a jikin Gawuna kuma akwai ta a jikin Garo, don haka a iya tunanin sa da ganin sa kamata yayi aƙara basu dama, inda ya ƙara da cewa “is a respect for APC ma tace tayi maintaning wannan ticket ɗin”
A ƙarshe yayi addu’ar fatan Allah Ya kauda duk wani mishkila da tarnaƙi da zai iya taɓa wannan tafiya ta Gawuna-Garo mai ɗumbun alkairai, Allah Ya kuma basu gagarumar nasara da sauran duk kujerun Jam’iyyar APC Ya ƙara zaunar da jihar mu da ƙasar mu lafiya da yalwar arziƙi.
Abubakar Musa DK
Media Aide to H.E Dr. Nasiru Gawuna