FB IMG 1780087498116

“Kai ma ka taba zama yaro na a siyasa” — Ganduje ya mayar wa Kwankwaso martani

 

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shima ya taba kasancewa “yaron sa” a fagen siyasa, yana mai cewa babu bukatar ‘yan siyasa su rika karkatar da tarihi ko rage dangantakar da ta dade zuwa kalaman “ubangida da yaro”.

 

Ganduje, wanda ke a ƙasar Saudiyya domin aikin Hajji, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin sa ta hannun Shugaban Ma’aikatarsa, Comrade Muhammad Garba, a ranar Juma’a.

 

A martanin da ya mayar kan kalaman da ake alakantawa da Kwankwaso, Ganduje ya ce siyasa tana ginuwa ne a kan alaƙa, goyon baya, sadaukarwa da kuma jagoranci, yana mai jaddada cewa babu wani babban ɗan siyasa da bai ci gajiyar taimakon wani a rayuwarsa ba.

 

A cewar sanarwar, Ganduje ya tuna cewa yana daga cikin wadanda suka taimaka wajen tasowar siyasar Kwankwaso tun da farko, musamman a lokacin zaɓen Majalisar Tarayya da ya kai shi mukamin Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai (Deputy Speaker).

 

“Wannan lokacin, Ganduje na da cikakken ikon kiran Kwankwaso yaron sa na siyasa, saboda ya ba shi goyon baya na ɗabi’a da na kuɗi, tare da tsayawa tare da shi a wancan lokaci,” in ji sanarwar.

 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa tun kafin wannan lokaci, lokacin da Ganduje ke aikin gwamnati a FCT sannan daga baya ya zama Kwamishina a Jihar Kano, Kwankwaso na yawan zuwa ofisoshin sa a Abuja da Kano domin ganawa, har ma yana iya jira na dogon lokaci kafin a gan shi.

 

Ganduje ya ce babu amfani a rika dawo da irin waɗannan batutuwa a siyasar yau, musamman a lokacin da ya kamata a mayar da hankali kan shugabanci da ci gaban al’umma.

 

Haka kuma, ya sake waiwayar tarihin siyasar Kano na shekarar 1998, inda ya ce da dama sun san cewa shi ne ya lashe zaben fidda gwani na gwamna a wancan lokaci, amma dattawan siyasa suka roƙe shi ya sauka domin haɗin kai, ya kuma amince ya zama mataimakin gwamna tare da Kwankwaso.

 

Sanarwar ta ce duk da irin wannan tarihi, su biyun sun yi aiki tare a matsayin gwamna da mataimaki daga 1999 zuwa 2003, sannan kuma daga 2011 zuwa 2015, a matsayin abokan siyasa da suka haɗa kai wajen ci gaban Jihar Kano.

 

Ganduje ya kuma yi tsokaci kan Gwamna na yanzu, Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa duk da ya taba kasancewa mataimaki ga Kwankwaso, a yau shi ne zababben gwamna kuma ya kamata a ba shi daraja da mutuncin ofishin da yake rike da shi.

 

Ya kara da cewa siyasa ba kamata ta kasance ta neman fifiko ko nuna iko ba, yana mai cewa kamar yadda uba zai iya renon yaro har ya zarce shi a matsayi, haka tsarin shugabanci yake a rayuwa.

 

A karshe, Ganduje ya yi kira ga ‘yan siyasa a Kano da su guji kalaman rarrabuwar kai, su mayar da hankali kan zaman lafiya da ci gaban jihar.

 

Ya kuma roki magoya bayan bangarori daban-daban da su kwantar da hankali, su guji tayar da zaune tsaye kan musayar kalaman da ke faruwa tsakanin shugabannin siyasa.

 

COMRADE MUHAMMAD GARBA

Babban Sakataren Yada Labarai ga Tsohon Shugaban APC na Ƙasa

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version