FB IMG 1771005913559

Wata kotu a Kano ta yanke wa jarumar Kannywood, Samha Inuwa, hukuncin daurin watanni shida

Mai shari’a S.M. Shuaibu na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, a ranar Juma’a, 13 ga Fabrairu, 2026, ya sami Sa’adatu Mohammed Inuwa (wadda aka fi sani da Samha) da laifi tare da yanke mata hukuncin daurin watanni shida bisa laifin wulakantawa da lalata takardar Naira.

An gurfanar da jarumar ne a gaban kotu kan tuhuma guda ɗaya da ta shafi lalata kuɗin Najeriya, wanda ya saɓa da tanade-tanaden Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007.

Tuhumar da ake mata ta ce: “Ke Sa’adatu Mohammed Inuwa, a wani lokaci a shekarar 2022, a cikin hurumin wannan kotu mai daraja, kin lalata takardar Naira N1000 (Naira dubu ɗaya) wadda Babban Bankin Najeriya ya fitar ta hanyar face majina da hanci, wanda hakan ya saɓa da sashe na 21(1) na Dokar CBN ta 2007.”

Ms Inuwa ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi bayan an karanta mata tuhumar. Dangane da amsa laifin da ta yi, lauyan masu gabatar da ƙara, Musa Isah, ya gabatar da hujjojin shari’ar tare da roƙon kotu ta yanke mata hukunci da ya dace.

Jarumar ta roƙi kotu da ta tausaya mata, tana mai cewa wannan shi ne karo na farko da ta aikata laifi kuma ta nuna nadama kan abin da ta yi.

Daga nan ne Alƙali Shuaibu ya yanke mata hukuncin daurin watanni shida, tare da zaɓin biyan tara ta Naira dubu dari biyu (N200,000) kacal.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version