Screenshot 20251218 084014

Shugaba Tinubu Ya Soke Ƙarin Girma Har Ninki Biyu Da Ya Yi Wa Dogarinsa

Rahotanni na cewa shugaba Bola Tinubu ya warware ƙarin girma har ninki biyu da ya yi wa dogarinsa, Nuruddeen Yusuf, biyo bayan caccaka da ya sha daga sassa daban-daban na ƙasar.

Tinubu ya ɗaga Laftanar Kanar Yusuf zuwa muƙamin Birgediya Janar, lamarin da ya janyo gunaguni da cece-ku-ce a tsakanin al’ummar ƙasar.

Jaridar PREMIUM TIMES  ta ruwaito cewa wata majiya ta shaida mata cewa shugaban ya lashe aman nasa ne sakamakon ƙwararan hujjoji da aka gabatar masa.

Majiyar ta ce The matakin soke wannan ƙarin girma ya zo ne bayan tattaunawa da manyan hafsoshin soji, da jami’an tsaro.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version