
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ziyarci iyalan wadanda akayi yiwa kisan Gilla su 7.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero cikin jimami da kaduwa ya bayyana cewa wannan wani babban rashi ne ga al’umar Jihar kano da kasa baki daya.
Yace bisa la’akari da yanayi na zamani ya zama wajibi al’uma sai san zama jami’an tsaron kansu domin sa ido da tsare kansu da iyalansu da kuma “yan uwansu.
Alhaji Aminu Ado Bayero yabawa mutanen unguwa da suka bada hadin kai da taimako a lokacin da wannan al’amari ya faru.
Ya hakukutar da Magidancin da wannan al’amari ya faru ga iyalan nasa su 7 tareda da yin addu’ar Allah ya karbi shahadarsu ya cigaba da bashi juriya da Hakurin rashinsu.
Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a lokacin ziyarar Ta’aziyyar yana tareda Hakimansa da sauran Masoya inda suma suka jajanta tareda yin addu’oin samun rahamar Ubangiji.