- Ikramatu Sulaiman Mustapha

SARKIN KANO ALHAJI AMINU ADO BAYERO YA KARBI LAMBAR GIRMAMAWA IRINTA TA FARKO A TARIHIN NAJERIYA.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi lambar Girmamawar tareda yabo ne daga Kungiyar Tsofaffin Kansiloli dake Mazabu dubu 774 dake fadin tarayyar kasar Nan.
Karin karbar Lambar Girmamawar Mai Martaba Sarkin ya karbi bakuncin Kungiyar SEWA International Phinthropy (Indian International) bisa Jagorancin Mr. Biial JI, Sarkin yayi farin ciki da zuwansu bisa irin ayyukan da sukeyi, kasancewar mutane na kashe kudade da yawa Domin su koyo abubuwa a Kasashe waje amma gasu sunzo Domin su l koyyawa al’umar Jihar Kano.
Yace akwai tsohuwar dangantaka tsakanin kasar India da Najeriya musamman yadda wasu daga cikinsu suka koyar da ilimi da kuma yadda ake kallon fina finai da makamantasu.
Ya bada misali ga Ambasadan kasar Pakistan Phm. Ahmad Ibrahim Yakasai yace yana kawo abubuwan cigaba a masaurata da Jihar Kano da Najeriya duk kuwa da cewa Dan Najeriya ne Kuma Dan asalin Jihar Kano kazalika Hakimai a Masarautar Kano amma kasar ta yadda dashi a matsayin wakilinta, ya godewa Allah da kokarinsa tareda fatan wannan dangantaka zata cigaba.
Ya godewa bakin da sukazo bisa Jagorancin Hajiya Hadiza tareda basu tabbacin hadin Kai na masarautar Kano tareda fatan zasu cigaba da kawo wa Jihar Kano abubuwan cigaba.
A nasa jawabin Shugaban Kungiyar ta SEWA International Phinthropy (Indian International) Mr. Biial JI yace sunzo ne domin su gabatar da kansu ga Mai Martaba Sarki tareda neman sa musu albarka a cikin ayyukan da sukayi.
A wani cigaban Kuma Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Bayero ya karbi bakuncin Kungiyar Kansiloli ta Kasa a fadarsa.
Sarkin yace a lokacin da suke a matsayin Hakimai Kuma suka zauna a Kananan Hukumomi daban daban sun san irin gudunmawar da Kansiloli suke bayarwa tareda shugabannin Kananan Hukumomi wajen cigaban aluma.
A don haka ya bukaci yan Kungiyar su cigaba da bayar da irin wannan gudunmawar duk kuwa da cewa basa kan mukamansu.
Ya gode musu bisa lambar Girmamawa da suka bashi tareda da basu tabbacin dukkan goyon bayansa da hadin Kai a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
A lokacin da da yake gabatar da Lambar Girmamawar tareda jawabinsa Shugaban Kungiyar Tsofaffin Kansilolin na Kasa Ambassador Auwal Kasim yace wannan itace Lambar yabo da Girmamawar ta farko da suka taba bawa wani shugaba ko jagora a Najeriya.
Yace sun bawa Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero lambar Girmamawar ne Saboda karamcinsa ga al’uma da rashin nuna bambanci ga kowanne jinsi da bin umarnin shugabanni da ladabi da biyayya da Kuma uwa uba Hakurinsa da Juriya akan dukkannin al’amura na rayuwa.
Kungiyar tayi fatan alheri ga Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero tareda addu’ar neman Allah ya cigaba da dafa masa a dukkan abubuwan da yasa a gaba.
Sa Hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Sakataren Yada labarai na Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL.
27/08/2025
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko abknaisa100@yahoo.com