
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’uma musamman wadanda Allah ya horewa su dunga aiwatar da ayyukan alheri ga jama’arsu musamman ta hanyar gina makarantun islamiyya domin amfanar ilimin yara masu tasowa.
Alhaji Aminu Ado Bayero yayi wannan kiran ne lokacikin da yake Bude sabuwar makarantar islamiyya da primary a Unguwar Yakasai dake cikin birnin Kano.
Makarantar wadda Perm. Ahmad Ibrahim Yakasai ya gina kuma ya bayar da ita Wakafi ga Mahaifiyar sa Hajiya Asma’u Ibrahim Yakasai, sarkin ya bayyana farin cikinsa da wannan abun alheri.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’ar Allah ya kai ladan wannan kyakkyawan aikin alheri a gareta, ya kuma yi addu’ar Allah ya bayar da ladan da yayi alkawari bayarwa ga duk wadanda sukayi irin wannan aikin alheri.
Bisa rakiyar dumbin al’umar jihar Kano masoya da magoya bayan mai Martaba sakin an kammala taron cikin farin ciki da walwala tareda addu’oi ga Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero wadanda al’uma keyi masa na fatana alheri.
Sa hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Sakataren Yada labarai na Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL.
5/10/2025