
Anyi kira ga Gwamnatin Tarayya data bada Umarnin Sakin Sheikh Sani Khalifa Zaria da aka tsare yanzu haka yake hannun Jami’an Tsaro.
Wannan kira na kunshe ne cikin wata sanarwa daga Majalisar Shura Atba,u Liddarikatut Tijjaniyya Wal Faira dauke da sa hannun Shugaban Majalisar Sheikh Yusuf Ahmad Gabari.
Sanarwar tace cigaba da tsare shi na tsawon kwanaki ba tareda kaishi kotu ba idan har an tabbatar da Zargin da akeyi masa ya saba da dokar Kasa.
A don haka ne Majalisar take bukatar ayi masa Adalci ko Kuma idan ba’a sameshi da laifi ba to a sakeshi ya dawo cikin iyalansa da Kuma almajiransa.
Majalisar Shura Atba,u Liddarikatut Tijjaniyya Wal Faira ta Bukaci Tijjanawa da Sauran al’umar Musulmi su cigaba da addu’a domin samun mafuta akan wannan al’amari.