Sanarwar ta fito ne daga shugabannin ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin shugaban ARD-FCT, Dr. George Ebong, wanda ya bayyana cewa matsalolin da suka haddasa yajin aikin sun haɗa da:
Karancin ma’aikatan lafiya
Kayan aiki marasa inganci
Matsin lamba ga likitoci wajen gudanar da ayyuka
Rashin biyan alawus na musamman
Dr. Ebong ya ce yawancin likitoci suna tilasta gudanar da aiki a sassa da dama lokaci guda, saboda ƙarancin ma’aikata, abin da ke haifar da gajiya da kuma barazana ga ingancin kulawar lafiya da ake bai wa marasa lafiya.
A cewarsa, tun a watan da ya gabata ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta ɗauki mataki kan waɗannan matsaloli, amma har yanzu ba a ga sauyi ba.
Ƙungiyar ta yi gargadi cewa idan aka ci gaba da yin watsi da bukatunsu, hakan na iya jefa tsarin kiwon lafiya gaba ɗaya cikin mummunan rikici a Babban Birnin Tarayya.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

