IMG 20251007 WA0160

An karrama Jihar Kaduna da lambar yabo ta Gwamnati Mafi Goyon Bayan Mata da Iyali wanda kungiyar Muryar Mata ( VOW) ta bashi.

Kungiyar tace Wannan karramawar tana girmama jihohi da cibiyoyi da ke nuna gagarumin kishin inganta rayuwar mata ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen da suka mayar da hankali kan karfafa mata.

Tace vaben Kaduna ya nuna yadda jihar ke gaba wajen kafa tsarin mulki mai kula da bambancin jinsi karkashin jagorancin Gwamna Sanata Uba Sani.

Daga cikin muhimman ayyukan da masu shirya taron suka jaddada akwai amincewa da baiwa mata mikamai masu gwavi da kuma kafa Sashen Kula da Bambancin Jinsi a Hukumar Siyan Kayan Gwamnati ta Jihar Kaduna (KADPPA).

Haka kuma an kafa wani sashi a cikin KADPPA domin tabbatar da aiwatar da tsarin da ke tabbatar da daidaito a tsakanin ma’aikatun gwamnati (MDAs).

A cikin jawabinta wajen taron, Dakta Nita Byack George, shugabar gudanarwa kuma mashahuriyar mai fafutukar kare hakkin mata ta yaba wa Gwamna Uba Sani, bisa hangen nesa da jajircewarsa wajen saka manufofin da ke karfafa mata cikin tsarin mulki da gwamnati.

Ta ce: “A matsayina na wadda ta shafe shekaru ina fafutuka kan kiwon lafiya, karfafa mata da shigar da su cikin jagoranci a matakan kasa da na duniya, ina farin cikin ganin yadda gwamnatin Kaduna ke aiwatar da tsarin mulki mai kula da bambancin jinsi cikin zahiri.”

Dakta George ta yaba da gyare-gyaren da Kaduna ke yi wajen karfafa mata, tana mai cewa hakan ya zama abin koyi ga sauran jihohi a fadin Nijeriya.

Ta qara da cewa: “Wadannan shirye-shirye sun nuna cewa Kaduna ba kawai magana take yi akan daidaito ba; tana aiwatar da shi ne a aikace , Gwamnatin Sanata Uba Sani ta zama abin koyi ga sauran jihohin Nijeriya.”

Taron na kungiyar (VOW), wanda shi ne babban dandali na qasa wajen bunkasa daidaito da hada kai tsakanin jinsi, ya tattaro wakilai daga gwamnati, kungiyoyin fararen hula, abokan ci gaba da kuma vangaren masu zaman kansu.

Wannan karramawar ta kara tabbatar da matsayin Jihar Kaduna a matsayin gwamnati mai kishin jama’a, wadda ke mayar da hankali wajen karfafa mata, bunkasa tattalin arzikin gida, da kare walwalar iyali ta hanyar tsare-tsare masu ma’ana da sauye-sauyen da ke tabbatar da daidaito tsakanin jinsi a fadin
Kasar.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version