
Gwamnatin Ƙasar Chadi Ta Ƙaryata Labarin Da ake Yaɗawa Cewa Ta Rufe Iyakokin Ta Saboda Barazanar Da Trump Yayi Na Kawo Hari Nigeriya
Babban Jami’in Ƙasar Chadi Dake Ƙasar Nan Mai Suna Dr. Umar Tahir Attayib Shine Ya Bayyana Hakan Yayin Zantawa Da Manema Labarai, Yana Mai Cewa Maganar Da ake Yaɗawa Bata da Tushe Ballantana Makama
Ya Ci-gaba Da Cewa Daman akwaibHaɗin Guiwar Jami’an Tsaron kasashen Tafkin Chadi a Iyakokin Ƙasashen Nan Domin Tabbatar Da Tsaro Wanda Kuma Da amincewar Duka wadannan Kasashe
Dan Haka Ya Bukaci Al’ummar Ƙasar Nan Suyi Watsi Da labarin Yana Mai cewa Na Kanzon Kurege ne
Ya kuma Kara Da Cewa abinda Yake Faruwa a Ƙasar nan na Matsalar Tsaro bashi da alaƙa da Addini Dan Haka Yace Maimakon barazanar Da Trump Yayi, Kamata Yayi Ya Taimakawa Nigeriya Da Kayan aiki da Za su Fatattaki Masu tayar Da Kayar Baya a cewar Dr Umar Tahir attayib Babban Jami’in Ƙasar Chadi Dake Jihar Borno