
Tsohon Kwamishinan Ganduje ya zargi gwamnatin Kano da kin aiwatar da kasafin kudin 2025 yadda ya kamata
Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labaran Kano a mulkin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Malam Muhammad Garba, ya zargi gwamnatin Kano da rashin aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025, musamman a bangaren ma’aikatar ruwa.
A cewar Muhammad Garba, koma bayan ayyukan samar da ruwa a jihar na da nasaba da ƙarancin kashe kuɗin da ma’aikatar da hukumar samar da ruwa suka samu.
Sai dai a martanin sa, Kwamishinan Ruwa na Kano, Malam Umar Haruna Muhammad Doguwa, ya ce zarge-zargen tsohon kwamishinan ba su da tushe. Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta tarar da nauyin bashin wutar lantarki da kuma lalacewar wasu cibiyoyin ruwa tun daga gwamnatocin baya.
Doguwa ya nuna cewa gwamnatin Kano ta fara gyaran manyan cibiyoyin samar da ruwa, samar da sabbin injinan tura ruwa, da tabbatar da biyan kuɗin wutar lantarki da kayan tsaftace ruwa domin inganta hidimar ruwa ga al’umma.
Zarge-zargen bangarorin biyu sun nuna sabani a ra’ayi game da yadda ake tafiyar da ayyukan ma’aikatar ruwa da kuma aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025.