Screenshot 20250928 233636 Samsung Internet

Gwamnatin Tarayya ta shiga tsakani a rikicin masana’antu da ya kunno kai tsakanin ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta ƙasa (PENGASSAN) da kuma hukumar Matatar Fetur ta Dangote, bayan sanarwar ƙungiyar na shirin fara yajin aiki a faɗin ƙasa daga Litinin, 29 ga Satumba, 2025.

A cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Ƙwadago, Patience Onuobia, ya fitar a ranar Lahadi, Ministan Ƙwadago da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyadi, ya roƙi PENGASSAN da ta dakatar da shirin yajin aikin.

Dingyadi ya bayyana cewa ma’aikatarsa ta gayyaci shugabannin PENGASSAN da kuma hukumar Matatar Dangote zuwa wani gaggawar zaman sulhu da za a gudanar a ofishinsa ranar Litinin.

Ya jaddada muhimmancin tattaunawa, yana mai gargaɗi cewa yajin aiki a ɓangaren man fetur na iya jawo mummunan tasiri ga tattalin arzikin ƙasa da tsaron ƙasa baki ɗaya.

“Ina roƙon ɓangarorin biyu su yi la’akari da muhimmancin bangaren man fetur ga ƙasa. Idan aka shiga yajin aiki, za a yi babban asarar kuɗi, kuma zai ƙara jefa ‘yan Najeriya cikin wahala tare da barazana ga tattalin arziki da tsaron ƙasa,” in ji Ministan.

Ministan ya bukaci PENGASSAN da ta janye yajin aikin da ta sanar, tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da jajircewa wajen warware rikicin, domin amfanin ƙasa da kuma gamsar da dukkan ɓangarorin

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version