Snapchat 1866391408

Gidan Radiyon Guarantee ya Jaddada Kudurin yin aiki tare da Gwamnatin kano domin cigaban Jihar – GM Kofar Naisa

Shugaban Tashar gidan Radiyon Guarantee dake Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya jaddada kudurin tashar nayin aiki tareda Gwamnatin jihar Kano.

Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin tawagar Mai Bawa Gwamnan Kano Shawara akan yada manufofin Gwamnati Hajiya Aisha Ahmad Tamburawa a ofishinsa.

Kofar Naisa yace babu wata kafar yada shirye shirye ta Radiyo da zata cigaba ba tareda samun hadin kan Gwamnati ba, kamar yadda itama Gwamnatin bazata samu cigaban da take bukata ba tareda hadin kan kafofin gidajen Radiyo ba.

Ya bayyana cewa dukkaninsu abokan tafiyar juna ne, domin sai da kafofin gidajen radiyon al’uma zasu san irin aikace aikacen da Gwamnati ke aiwatarwa.

Shugaban tashar gidan Radiyon Guarantee Kofar Naisa ya bukaci Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bawa kafofin gidajen Radiyon hadin kai da goyon baya domin cimma bukatar da akasa a gaba.

A nata Jawabin Mai bawa Gwamnan Kano Shawara akan Yada manufofin Gwamnati Hajiya Aisha Ahmad Tamburawa tace taje gidan Radiyo Guaratee ne domin kulla kyakkayawar alaka tsakani Gwamnatin Kano da gidan Radiyon.

Hajiya Aisha Tamburawa tace Gwamnatin Abba Kabir Yusuf a shirye take tayi aiki kafada da kafada domin inganta aikin gidajen radiyo kasancewar sune ke isar da sahihin sako tsakanin gwamnati da al’uma.

Dagana ta bukaci hadin kai da goyon bayan gidan Radiyon Guarantee domin samun nasarar da ake bukata.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version