
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin ya baiyana hakan ne yayin rabon tallafin karatu ga ɗalibai 1000 ƴan yankin Kano ta Arewa da ke Jami’ar Ilimi ta Maitama Sule a jihar Kano.
Da ya ke jawabi a wajen taron, Sanata Barau ya baiyana cewa jami’ar a da, kwalejin ilimi ce aka maida ta jami’a a lokacin mulkin Jonathan amma daga bisani aka soke.
“Da na zama mataimakin shugaban majalisar dattawa, sai na tuntubi Tinubu da ƙudirin a sake dawo da ita a matsayin jami’a. Na fara yi masa bayani, kan na gama ma ya rattaba hannu ya ce kawai ya amince.
“Duk rokon da na mika masa na ayyukan cigaba a Kano duk ya amince da su,”
Sanata Barau ya ce lokaci ya yi da al’ummar Kano da ma Arewa baki ɗaya za su saka wa Tinubu da alherin da ya yi musu idan zaɓen 2027 ya zo