Dakarun Nijeriya sun hallaka manyan kwamandojin ISWAP 5 da mayaƙan su 45 a Borno da Yobe
Manyan kwamandojin kungiyar yan ta’adda ta ISWAP biyar ne aka tabbatar da sun rasa ransu a yayin da sojojin rundunar Hadin Kai suka dakile hare haren ‘yan ta’adda a Borno da Yobe a wani al’amari da majiya daga rundunar soji ta bayyana da babban koma baya ga ‘yan ta’adda.
Acewar rahotan Zagazola Makama, manyan kwamandojin da aka kashe sun hada da; Ari Kolo da Ya Muhammad da Abu Aisha da Hamzalah da Abu Rijal.
Sun gamu da ajalinsu ne a safiyar yau Alhamis a garin Dikwa da Mafa da Gajibo da Katarko.
Bayanai sun bayyana cewa mayakan sun mutu ne a yayin da suka kai mafarki ga Sojoji.
Acewar sanarwar daga rundunar sojin hadin gwiwa dake aiki a yankin Arewa maso Gabas, an kashe ‘yan ta’adda 62.
Laftanar Kanal Sani Uba, jami’in yaɗa labarai na rundunar ya ce an fara fatattakar mayakan ne tun tsakar dare inda Sojojin ƙasa ke samun tallafi daga jiragen yaƙi.
Sannan ya ce sojoji sun kwato bindiga kirar AK-47 har guda 38 da sauran makamai.

