
Sanatan Amurka daga Jihar Texas, Ted Cruz, ya sanar da shirin gabatar da wata doka da za ta hukunta ‘yan siyasar Najeriya da suka kafa ko suka goyi bayan dokokin Shari’a da kuma na cin mutuncin addini (blasphemy laws) a jihohinsu.
A cewar rahotanni daga majalisar dattawan Amurka, wannan doka za ta bai wa gwamnatin Amurka damar sanya takunkumi (sanctions) kan duk jami’an Najeriya da aka tabbatar sun aiwatar ko suka goyi bayan waɗannan dokoki da ake ganin suna tauye yancin addini.
Ted Cruz ya ce:
“Najeriya na fuskantar babban ƙalubale na yancin addini, kuma za mu tabbatar da cewa waɗanda suka kafa dokokin da ke takura wa mutane saboda addininsu sun fuskanci hukunci.”
A lokacin da ake kafa Shari’a a Arewa, an fara aiwatar da ita ne a Jihar Zamfara ƙarƙashin tsohon gwamna Sanata Ahmad Sani Yarima (Bakura), wanda shi ne ya kaddamar da dokar a hukumance a shekarar 2000.
Daga nan ne kuma tsohon gwamna Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bi sahu ya kaddamar da ita a Jihar Kano da wasu ƙarin jihohi a Arewa maso yamma.
Yanzu dai, bayan Donald Trump ya sake jefa Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da cin zarafin Kiristoci, Sanata Cruz na neman a tafi gaba — a binciki kuma a hukunta ‘yan siyasar da suka kafa irin waɗannan dokoki.
Masana harkokin diflomasiyya sun ce wannan mataki zai iya jawo ƙarin hatsaniya tsakanin Najeriya da Amurka, musamman ganin cewa dokar Shari’a tana da tushe na siyasa da addini a Arewa.
Mikiya Hausa.