
Tuni dai aka kira shugaban jam’iyyar a Kano, Abdullahi Ganduje, daga tafiyar da ya yi zuwa Dubai, a daidai lokacin da aka nemi shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas, ya takaita tafiyarsa ta aikin hajji don bai wa gwamnan katin zama dan jam’iyyar APC a gundumarsa ta Diso da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano a wannan makon.