
kamfanin samar da kayayyaki na Najeriya, BUA Group, ya mayar da martani game da wani mummunan harin da aka kai kusa da masana’antarta ta siminti da ke Okpella, jihar Edo, wanda ya yi sanadin kashe jami’an hukumar tsaro ta NSCDC takwas da wani direban farar hula tare da yin garkuwa da daya daga cikin ma’aikatanta na kasashen waje.
Kamfanin, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’an hukumar a ranar Lahadi ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tausayi tare da jaddada kudirinsa na tallafawa jami’an tsaro.
“BUA yayi matukar bakin ciki da harin da aka kai ranar Juma’a, 5 ga Satumba, 2025, inda jami’an tsaro 8 na hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) da wani direban farar hula suka rasa rayukansu a kusa da cibiyar mu ta Okpella a jihar Edo.
“Muna mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu, NSCDC, da gwamnatin Najeriya, muna kuma yi wa jami’an da suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.
“Mun lura matuka da yadda aka yi garkuwa da wani dan kasar waje, duk da cewa an kubutar da wasu mutane hudu ba tare da sun ji rauni ba, muna kuma hada kai da jami’an tsaro don ganin an dawo da wadanda aka sace cikin koshin lafiya da kuma gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyen aikin a gaban kuliya.
“Tsaron mutanenmu, abokanmu, da kuma al’ummomin da suka karbi bakuncinmu ya kasance mafi muhimmanci. Wannan bala’in tunatarwa ne mai raɗaɗi game da sadaukarwar da jami’an tsaronmu ke bayarwa a kullum. Ba za a taɓa mantawa da jaruntakarsu ba.”
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com