1758881457622.Screenshot 20250926 111020

“AN YANKA TA TASHI”  Yanzu haka dai an gano cewa  Kano ce ta 29 a jarabawar NECO ta 2025, ba ta ɗaya ba kamar yadda gwamna Abba K. Yusuf ya yi ikirari

Ba kamar yadda gwamnan Kano Abba Yusuf ya bayyana cewa wai jihar Kano ce ta yi zarra a jarabawar kammala babbar sakandare, NECO a jarabawar bana, an gano cewa hakan ba daidai bane.

 

Gwamna Abba ya yi kurin cewa saboda irin maida hankali da gwamnatinsa ta yi na inganta fannin ilimi a jihar ne ya sa ɗaliban jihar suka yi nasara a jarabawar ta bana.

 

Gwamna Yusuf ya kara a cewa jihohin Legas da Oyo ne suka zo na biyu da uku bisa ga Sakamakon jarabawar da aka fitar.

 

Sai dai kuma binciken kwakwaf da PREMIUM TIMES ta gudanar domin tantance kalaman gwamnan, an gano cewa ba jihar Kano bace ta zo na ɗaya a jerin jihohin Najeriya bisa sakamakon da NECO ta fitar.

 

Abinda aka gano shine Jihar Kano ce ta zo na ɗaya a yawan ɗaliban da suka rubuta jarabawar, domin ita kaɗai tana da kashi 10 cikin 100 na yawan ɗaliban da suka rubuta jarabawar a duk Najeriya.

 

Binciken ya nuna cewa jihar Kano ce ta zo na 29 cikin Jihohi 37 har da Abuja a nasarar da jihohi suka samu a sakamakon jarabawar NECO ɗin.

 

Jihar Kano na sama da jihohi 8 ne daga yankin Arewa da suka haɗa da jihohin Yobe, Adamawa, Plateau, Borno, Jigawa, Katsina, Zamfara, da Sokoto.

 

Bisa ga sakamakon da hukumar ta fitar, sama da kashi 50 cikin 100 na ɗaliban jihar Kano da suka rubuta jarabawar NECO sun faɗi jarabawar, domin duk basu yi ci lissafi da Turanci ba wanda shine muhimman darussan da ake buƙata domin samun gurbin shiga makarantun gaba da sakandare.

 

A ƙididdige, jihar Kano ce ta kowacce jihar faɗuwa jarabawar NECO a bana idan aka yi la’akari da yawan ɗaliban da suka rubuta jarabawar da kuma yawan waɗanda suka ci jarabawar.

 

Jihohi 10 da suka fi faɗi jarabawar NECO a Najeriya

 

Daga na 28 zuwa na 37.

 

28. Bauchi – 52.62 per cent

29. Kano – 49.84 per cent

30. Yobe – 48.13 per cent

31. Adamawa – 47.99 per cent

32. Plateau – 46.46 per cent

33. Borno – 44.72 per cent

34. Jigawa – 43.81 per cent

35. Katsina – 42.89 per cent

36. Zamfara – 42.12 per cent

37. Sokoto – 35.00 per cent

 

Jihohi 10 da suka fi yin nasara jarabawar NECO 2025

 

Abia – 83.31 per cent

 

Imo – 83.09 per cent

 

Ebonyi – 80.60 per cent

 

Anambra – 76.80 per cent

 

Bayelsa – 73.88 per cent

 

Delta – 73.10 per cent

 

Osun – 72.64 per cent

 

Ogun – 72.21 per cent

 

Lagos – 71.76 per cent

 

Ekiti – 68.50 per cent

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version