IMG 20260125 WA0149

Ambasada Yerima Usman Shettima Ya Nuna Tausayi ga Al’ummar Kurmin Wali, Ya Yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna kan Ƙoƙarin Tsaro

 

Daga Shehu Usman Yahaya

 

Ambassador Yerima Usman Shettima ya bayyana matuƙar tausayi da alhini ga al’ummar ƙauyen Kurmin Wali da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru, biyo bayan sace sama da mutane 100 masu bauta a yankin.

 

A cikin wata sanarwa da ya fitar Wanda aka rabawa manema labarai a Kaduna, Ambasada Shettima ya bayyana lamarin a matsayin abin tausayi da takaici, yana mai cewa hakan wata babbar tunatarwa ce kan ƙalubalen tsaro da ke fuskantar al’umma a faɗin jihar da ma ƙasar nan baki ɗaya.

 

Akan hakan Ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika, yana mai jaddada cewa irin wannan ta’addanci na barazana ga zaman lafiya, haɗin kai da cigaban tattalin arzikin Jihar Kaduna.

 

Ambasada Shettima, wanda ke ɗaya daga cikin masu neman takarar kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwan waɗanda abin ya shafa, tare da yin addu’ar Allah Ya sa a sako dukkan waɗanda aka sace cikin gaggawa da lafiya.

 

Ya kuma yabawa da jajircewar al’ummar Kurmin Wali bisa yadda suka fuskanci wannan mawuyacin hali.

 

Haka zalika, Shettima ya yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa gaggawar dauki da ya Kai ga al’ummar yankin da kuma ci gaba da ƙoƙarinsa wajen magance matsalolin tsaro a faɗin jihar.

 

Ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya nuna cikakken ƙuduri na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da aiwatar da salon mulki mai mayar da hankali kan jama’a, musamman ta hanyar haɗin gwiwa da jami’an tsaro da kuma al’ummomin da abin ya shafa.

 

A cewarsa, jagorancin Gwamna Uba Sani ya nuna sabon ƙwazo wajen tinkarar matsalar tsaro ta hanyar ayyukan tsaro na bayanan sirri, haɗin gwiwa da hukumomin tsaro, da kuma tsarin mulki mai bai wa jin daɗin al’umma fifiko.

 

Ambasada Shettima ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara zage damtse wajen ceto waɗanda aka sace tare da cafke masu hannu a wannan aika-aika domin hukunta su bisa doka.

 

Ya kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu lura da abin da ke faruwa a yankunansu, tare da bai wa hukumomin tsaro cikakken goyon baya, yana mai jaddada cewa haɗin kan jama’a da gwamnati shi ne mabuɗin magance matsalar satar mutane da ‘yan bindiga.

 

Ambasada Shettima ya bayyana cewa burinsa na neman kujerar Sanata ya samo asali ne daga aniyarsa ta bayar da gudummawa mai ma’ana ta fuskar manufofi da ayyukan majalisa da za su ƙarfafa tsaro, bunƙasa cigaba, da inganta rayuwar al’umma.

 

Yayi addu’ar zaman lafiya ga al’ummar Kurmin Wali da Jihar Kaduna, dama Nijeriya baki ɗaya, tare da nuna fata cewa ta hanyar shugabanci nagari da haɗin kai, za a samu mafita mai ɗorewa ga matsalolin tsaro

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version