IMG 20251030 154824

Wani Dattijo a yankin Kuma Turakin Sharifan Ungogo Sharif Saihan Hambali shine ya bayyana hakan ga wakilinmu a lokacin da yake duba yadda aikin titin zai kasance.

Sharif Saihan Wanda Kuma shine Daraktan Makarantun Ummulkhairi yace Sheikh Abdulkadir Jiyali Kurna yayi abun a yaba matuka bisa wannan aiki da ya kawo Wanda Sanatan Kano ta Arewa Sanata Barau Jibrin ya dauki nauyi.

Yace wannan aikin titin zai rage wahalhalu matuka tsakanin wadanda suke zirga zirga daga Kurna Farin Bene zuwa Kurna Babban Layi.

Dattijo Sharif Hambali yace a baya al’umar wannan yanki zunsha fama tareda wahala ta yadda basa iya gabatar da wasu al’amura na yau da Kullum.

Yana Mai cewa Amma a yanzu suna Mai godewa Allah da suka samu wannan aiki da Sheikh Abdulkadir Jiyali Kurna ya kawo musu tareda bukatar Al’uma su bada dukkan hadin Kai domin gudanar da aikin cikin nasara.

Al’umar yankin Kurna Farin Bene sunyi addu’oi na Musamman ga Sanata Barau Jibrin da Sheikh Abdulkadir Jiyali Kurna bisa wannan aikin cigaba da aka kawo musu yankinsu.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version