IMG 20251101 WA0026

Tsohon Babban Kwantrola Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), Muhammad Babandede, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ƙarfafa dangantaka ta aiki tsakanin Hukumar Kwastam ta Ƙasa (NCS) da Hukumar Shige da Fice (NIS) domin inganta tsaron iyakoki da kyautata tsarin gudanar da ƙasar.

 

Babandede ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da Migrationwatch Magazine, inda ya yi kwatancen yadda gwamnatin Amurka ta haɗa hukumar shige da fice da ta kwastam bayan harin 11 ga Satumba (9/11) domin ƙarfafa tsaron cikin gida.

 

Ya bayyana damuwarsa kan yadda a Najeriya, hukumar Kwastam da ta Shige da Fice ke aiki dabam-dabam, duk da cewa suna da ayyuka masu kama da juna.

 

“Duk lokacin da aka nemi su yi aiki tare, ɗaya daga cikinsu kan guji ɗaya,” in ji shi.

 

A cewarsa, motsin kaya da na mutane abu ne guda, musamman a yankin Afirka ta Yamma.

 

“Mutumin da yake ɗauke da kaya da wanda yake tafiya abu ɗaya ne, musamman a yankinmu. Ba za ka iya raba motsin kaya da motsin mutanen da ke ɗauke da su ba,” in ji Babandede.

 

Ya jaddada bukatar ƙulla haɗin kai da kirkire-kirkire tsakanin hukumomin biyu domin yaƙar manyan laifukan da ke ketare iyakoki.

 

“Ya kamata Hukumar Shige da Fice da ta Kwastam su zuba jari wajen ƙarfafa haɗin gwiwa a tsakaninsu, domin tabbatar da ingantaccen tsaron iyakoki da kuma nagartaccen tafiyar da harkokin gwamnati,” in ji shi.

 

Babandede ya kuma soki abin da ya kira “rashin kulawa mai tsanani” wajen fahimtar muhimmancin hijira a ci gaban ƙasa. Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da ake yi a Hukumar Shige da Fice, domin inganta hanyoyin kula da iyakoki da tsaron ƙasa.

 

“Iyaka ba wurin tsaro kaɗai ba ce, tana kuma da muhimmanci a fannin al’adu, tarihi da kasuwanci,” in ji shi, yana mai kira da a samar da yankunan kariya da kuma ƙara haɗin kai da ƙasashen makwabta.

 

Haka kuma, tsohon shugaban ya jaddada bukatar Najeriya ta samar da ingantacciyar manufar hijira ta ƙasa, wadda za ta binciki tasirin bakin haure ga tattalin arzikin ƙasa.

 

“Hijira muhimmin ginshiƙi ne na ci gaban ƙasa. Dole ne Najeriya ta kula da irin mutanen da take bari su shiga ƙasa da kuma waɗanda take bari su fita. Ya kamata mu tantance irin ayyukan da bakin haure ke yi da yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Haka kuma, dole ne mu dakile waɗanda ke kawo cikas ga ci gaban ƙasa,” in ji Babandede.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version