1758744041410.Screenshot 20250924 205911

Za a rufe kasuwanni a Ibadan domin bikin bada sandar sarauta ga Olubadan

Za a rufe dukkan kasuwanni a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Juma’a domin ‘yan kasuwa su girmama nadin Olubadan na 44 na Ibadanland, Oba Rasheed Adewolu Ladoja.

Jaridar LEADERSHIP ta rawaito cewa Babban Babaloja na Jihar Oyo, Asiwaju Yekeen Abass, ne ya bayar da umarnin, inda ya bayyana cewa rufe kasuwannin zai kasance alamar girmamawa ga sabon sarki.

Abass ya bayyana cewa dukkan kasuwanni da ke cikin kananan hukumomi goma sha ɗaya na Ibadanland, ciki har da na cikin birni da kewaye, za su dakatar da harkokin kasuwanci a wannan rana.

Babban Babaloja ya taya Oba Ladoja murna a madadin majalisar shugabannin kasuwa, shugabannin yankuna da kuma daukacin al’ummar ‘yan kasuwa a jihar Oyo.

Ya yi addu’ar samun zaman lafiya, wadata da mulki mai tasiri wanda zai kawo cigaba ga Ibadanland da jihar baki ɗaya.

Babban Babaloja ya kuma bukaci dukkan ‘yan kasuwa su halarci bukin nadin a Mapo Hall, inda ya jaddada muhimmancin nuna goyon baya da girmamawa ga sabon sarki na gargajiya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version