Shugaba Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Ɗaukar Ƴansanda 30,000

Shugaban Najeriya ya bayar da umarnin a dauki yan Sanda 30,000 bayan sace-sacen mutanen da aka yi a kwanakin baya bayannan.

Ofishin Shugaban kasar Bola Tinubu, ya kuma sanar da cewa duk jami’an tsaron da ke kare manya masu fada aji a kasar a mayar da su sauran fagen daga domin suje su cigaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar.  ‎

Wannan yunkurin ya zo ne bayan da yara 50 daga cikin fiye da 300 da aka sace a makarantar sakandire st Mary da ke jihar Neja suka kubuta daga hannun wadanda suka sace su.

Wakiliyar BBC ta ce an umarci makarantu a wasu sassan jihohin Najeriya da su rufe makarantun bayan sace sacen daliban da a ka yi a baya bayannan, sannan kuma bayan shafe mako guda a hannun masu satar mutane an sako mutum 38 da aka sace a wani coci a jiya Lahadi.

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version