
Murtala Sule Garo Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Yan Majalisu Biyu Na Jam’iyyar NNPP A Jihar Kano
Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a zaben shekarar 2023, Alhaji Murtala Sule Garo ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar Hon. Aminu Sa’ad Ungogo, dan majalisar jiha mai wakiltar Ƙaramar hukumar Ungogo da Hon. Sarki Aliyu Daneji, dan majalisar jiha mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birni, wadanda suka rasu a jiya Laraba Sa’o’i kasan tsakaninsu da juna.
“Hakika na kadu matuka da samun labarin rasuwar ‘yan majalisun jihar kano guda biyu, wadanda su ka rasu jiya Laraba”.
Garo ya kara da cewa; Tabbas wannan babban rashi ne, ba ga iyalansu kadai ba, har na ga daukacin al’ummar jihar Kano. Domin rashi ne da taba zukatan al’umma baki daya.
“Ina mika sakon ta’aziyya ga iyalai, yan uwa, abokan mu’amala, abokan siyasa da daukacin al’umma wannan jiha”.
Daga karshe ya kuma yi rokon Allah Madaukakin Sarki ya ji kansu da rahama, ya gafarta musu, ya baiwa iyalansu juriyar wannan rashi ya kuma sa Aljannatul Firdaus makomarsu. Amin.