
By. Ahmad Muhammad Sani Gwarzo Anipr.
KANANAN HUKUMOMIN GWARZO DA KABO SUN BAYYANA KOKARIN SU A BIKIN NUNA AL’ADU DANA KASUWANCI WANDA AKE GUDANARWA YANZU HAKA NAN A JIHAR KANO.
Ana samun kyakkyawar nasara daga ƙananan hukumomin Gwarzo da Kabo a yayin Bikin nuna Al’adun na Jihar Kano na bana, inda suka fito da bajintar su ta fannin noman zamani, nune-nunen kayayyakin gona, da kuma fasahar shiryawa da sanya kayayyaki cikin zamani, wanda hakan ya sanya su cikin jerin mafi kyawun mahalarta a bana.
Manoma da ’yan kasuwa daga ƙananan hukumomin biyu sun gabatar da kayayyakin Amfanin gonar su Wanda Suka noma Shi a Cikin Wannan damunar ta bana da suka haɗar da rogo, masara, gero, dawa, Kiwon Kaji, Talatalo, kifi da shinkafa, da sauran nau’o’in amfanin gona, waɗanda ke nuna yalwar arzikin noma da jajircewar jama’ar yankin wajen tabbatar da wadatar abinci a cikin jihar.
Yayin da yake ganawa da ’yan jarida a filin baje kolin al’adu da kasuwanci na Kano, wanda ya kafa kuma yake shugabantar Gidauniyar Dr. Ambassador Umar Shu’aibu Gwarzo, wato Dr. Umar Shu’aibu Gwarzo, ya yaba ƙwarai da yadda mahalarta daga kananan hukumomin Gwarzo da Kabo suka nuna bajinta da ƙwarewa wajen inganta kayayyakin Amfanin gonar su a matakin jiha.
> “kananan hukumomin Gwarzo da Kabo sun nuna abin koyi a wannan shekarar. Fasaharsu, ingancin kayayyaki, da yadda suka shirya su cikin tsarin zamani abin koyi ne ga sauran kananan hukumomi,”
— in ji Dr. Umar Shu’aibu Gwarzo.
Ya kuma ƙara da cewa, gidauniyarsa za ta ci gaba da haɗa hannu da Kananan hukumomin Gwarzo da Kabo domin ƙarfafa manoma, matasa, da mata wajen cimma ci gaba mai ɗorewa da dogaro da kai.
A nasa jawabin, Daraktan Tsare-tsare da Ci gaban Al’umma na Gidauniyar Dr. Ambassador Umar Shu’aibu Gwarzo, wato Dr. Baffa Datti Gwarzo, ya bayyana cewa duk da cewa gidauniyar ba ta gwamnati ba ce (NGO), tana aiki tare da gwamnati wajen kawo cigaba da bunƙasa rayuwar al’umma.
> “Manufar mu ita ce mu tallafa wa gwamnatin jiha wajen haɓaka al’umma ta hanyar ƙarfafa noma, ba da horo ga matasa, da inganta rayuwar jama’a. Idan muka haɗa kai, za mu iya cimma ci gaban da zai dore,”
— in ji Dr. Baffa Datti Gwarzo.
Wannan taron yana samun halartar ’yan kasuwa, manoma, ma’aikata, da jami’an gwamnati daga sassa daban-daban na jihar, wanda ya zama dandalin musayar al’adu, hulɗar tattalin arziki, da haɓaka sana’o’in gargajiya da zamani.
Gidauniyar Dr. Ambassador Umar Shu’aibu Gwarzo ta kuma sake jaddada aniyarta na ci gaba da tallafawa matasa, manoma, da al’umma baki ɗaya wajen cimma Nasara da walwala a fadin Jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

