1757865546627.Screenshot 20250914 164526

Hukumar Asibitin AKTH ta Bukaci KEDCO da ta mayar da Wutar Lantarki a Asibitin Domin Dakatar da Mutuwar Marasa Lafiya.

 

Hukumar Kula da Asibitin Koyarwa ta Aminu Kano (AKTH) ta yi kira ga Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki dake Kano wato (KEDCO) ya mayarwa da asibitin wutar lantarki domin kaucewa ci gaba da asarar rayukan marasa lafiya da kayan tallafi na rayuwa.

 

Hukumar ta yi alhinin rasuwar wasu majinyata da ke cikin mawuyacin hali bayan da KEDCO ta wutar lantarkin Asibitin duk kuwa kokarin da hukumar Asibitin keyi na kokarin biyan kudin wutar.

 

Asibitin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da shugabar sashen yada labarai, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar, ta ce asibitin a kai a kai yana biyan kudin wutar lantarki ga KEDCO daga kudaden shiga na cikin gida; sannan kuma ana amfani da wani bangare na irin wadannan kudaden shiga wajen siyan dizal don samar da wutar lantarki a wurin domin kara karfin wutar da KEDCO ke samarwa.

 

  1.  Hauwa Dutse ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai cewa, Hukumar ta AKTH ta yi kira ga KEDCO da ta tallafa wa ayyukanta na kiwon lafiya ga majinyata ta hanyar maido da wutar lantarki a Asibiti yayin da take daukar matakai na karya wasu kudade.
Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version