
DAWOWAR NAFISA ABDULLAHI…..
Tun jiya da Mallam Abdul amart yaje har iyapot rako Jaruma Nafisa Abdullahi sakamakon fara daukar shirin KADDARA da za’a fara yi ayau, kafofin sada zumunta suka dau dumi ba don komai ba sai dan ita kanta NAFISA ABDULLAHI (kazar Hausa) tana da nata mabiyan sosai wadanda sukayi kewarta musamman jimawa da akayi ba’a ganta ba cikin Fina finai, harma cikin series da ake yayi a masana’antar yanzu, tun bayan daina ganinta acikin Shirin Labarina datayi shekarun baya….
Babban abinda ze kayatar shine, ganin yanda manyan screen 📺 presence na arewa zasu bayyana acikin shirin, wato Ali Nuhu Mohammed, Adam A Zango da kuma ita kanta Nafisat Abdullahi.
Alaji tundaga 🇺🇸 America ta taho don daukar Wannan shirin, kada kuso jin kudin da wannan project din zeci….
Tunda naga marubucin Yakubu M. Kumo ne, naga mashiryin shirin Abdul Amart ne, naga kuma Falalu a dorayi shine daraktan shirin nasan tabbas makallata zasu nishadantu kuma su karu da wannan shiri, muna kyautata zaton wannan shirin ze ilimantar da makallata fiye da shirin MANYAN MATA.
Yau 11 ga watan December 2025 za’a fara daukar wannan shiri, inaiwa dukkan jarumai (cast) da ma’aikatan wannan shiri (crew) da sponsors hadi da partners na Wannan shiri fatan nasara.