IMG 20250828 WA0037

AN NADA SABON SARKIN ZURU

An bayyana Sabon Sarkin Zuru. Shi ne Alhaji Sanusi Mikail Sami, Sami Gomo na III.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na Jihar Kebbi Alhaji Abubakar Garba Dutsin-Mari ne ya sanar da hakan a hukumance a yau, Alhamis, a fadar Sarkin Zuru, wanda kuma ya mika takardar nadin da Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya sanya wa hannu.

Yayin gabatar da wasikar, Kwamishinan ya bayyana cewa nadin ya biyo bayan mika sunayen mutane uku da masu nada Sarki a masarautar Zuru suka mika wa Gwamna, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Gwamna Nasir Idris yayi amfani da ikon da aka ba shi ya amince da Alhaji Sanusi Mikail Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru, wanda yanzu aka amince da shi a matsayin Sarki ZURU Gomo na III.

Tun da farko, Sarkin Wasagu, Alhaji Muktari Musa, wanda ya rike mukamin mukaddashin sarki tun bayan rasuwar marigayin, ya karbi bakuncin sabon sarkin a hukumance tare da maraba da dukkan baki a fadar.

A nasa jawabin, sabon sarkin ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da kuma Gwamna Nasir Idris bisa amincewar da suka yi masa.

 

Ya kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu zaman lafiya da aminci da hadin kai, yana mai ba su tabbacin budaddiyar manufa da shugabanci mai dunkulewa.

Ya kuma yabawa Sarkin Wasagu bisa irin yadda yake gudanar da ayyukansa a lokacin rikon kwarya, ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafawa al’ummar Masarautar kamar yadda ya saba yi.

Ya bukaci al’ummarsa da su ba shi hadin kai da addu’a domin samun nasara.

A wata sanarwa da mai baiwa gwamnan jihar Kebbi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki ya fitar ta ce za a iya tunawa marigayi Sarkin Musulmi, Manjo Janar Muhammad Sani Sami (Gomo II) mai ritaya, ya rasu kwanan nan a wani asibiti da ke Landan, kuma an yi masa jana’iza a gidansa da ke Zuru.

Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko abknaisa100@yahoo.com

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version