Screenshot 20251124 165205

Amurka za ta bai wa Najeriya tallafin kayan tsaro da na leken asiri.

Fadar shugaban Najeriya ta ce Amurka ta tabbatar da shirinta na zurfafa hadin gwiwa a fannin tsaro da Najeriya, da ya hada da samar da ingantattun bayanan leken asiri da kayayyakin tsaro da kuma karfafa ayyukan da ake yi na yaki da ‘yan ta’adda da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a kasar.

Matakin ya biyo bayan ganawar makon jiya ne tsakanin wata tawagar manyan jami’an Najeriya da jami’an Amurka, kan zargin yi wa kiristoci kisan gilla.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version