
ILMIN FIRAMARE YANA DAYA DAGA CIKIN MATAKAN KOYAR DA YARA TARBIYYA TUN DAGA TUSHE
An bukaci sababbin malaman makarantun firamare da Gwamnatin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ta dauka aiki a karamar hukumar Rano da su zama masu koyar da kyakkyawar tarbiya ga yara.
Shugaban kwamitin kudi a majalisar dokokin jihar Kano, kuma mai wakiltar Karamar hukumar a majalisar, Alhaji Ibrahim Malami Rano ne ya bayyana bukatar yayin raba takardun daukar aikin koyarwa a makarantun firamaren yankin ga Malaman din-din da ‘yan BESDA wanda aka yi a dakin taron sakatariyar karamar hukumar da ke garin Rano.
Wannan na cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in yada labarai mai lura da kananan hukumomin shiyar Rano Malam Abdullahi Musa Gyadi Gyadi ya raba inda sanarwar ta kara da cewa karamar hukumar ta samu takardun daukar aikin malamai dari da hamsin wadanda suka hada da masu takardun daukar aikin na din-din su casa’in da biyu da ‘yan BESDA guda su hamsin da uku.
Alhaji Ibrahim Malami Rano yace idan malamai suka koyar da kyakkyawar tarbiya ga yaran makarantun firamare kuma iyaye na tallafawa a gida yaran za su tashi a matsayin masu biyayya da hali nagari abin alfahari.
Dan majalisar jihar, ya jaddada aniyarsa da ta Dan majalisar tarayyar yankin Alhaji Alasan Rurum da shugaban karamar, Malam Muhammad Naziru Ya’u Rano na ci gaba da tallafawa duk shirin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf na ciyar da ilmi da bunkasa rayuwar al’umar yankin da jiha baki daya.
Shugaban karamar hukumar ta Rano Malam Muhammad Naziru Ya’u Rano a jawabinsa ya bukaci wadanda aka rabawa takardun daukar aikin koyarwar da su godewa Allah da gwamnatin jiha da ‘yan majalisun jiha dana tarayya masu wakiltar yankin bisa tallafin da suka bayar don sama musu takardun dauka aikn.
Malam Muhammad Naziru Ya’u Rano ya bukaci wadanda aka dsuka aikin da su zama masu kwazo wajen gudanar da aikin su.
Sakataren ilmin karamar hukumar, Alhaji Sani Ibrahim Ya’u Rano ya bada tabbacin za su yi aiki tare da sababbin malaman tare da kira a gare su day su zama masu bada hadin kai da kyakkyawar gudunmwa don inganta ilmi a yankin.
Daya daga cikin wadanda aka dauka akin kuma shugaban kungiyar sababbin malaman na karamar hukumar ta Rano Malam Kamar Yusha’u Shangu a madadin sauran wadanda aka dauka akin koyarwar, ya yi godiya ga Gwamnatin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa yadda ta samar musu da aikin yi tare da alkawarin bada kyakkyawar gudunmwa don c gaban ilmi a karamar hukumar da jihar Kano baki daya.
Sa hannu
Abdullahi Musa Gyadi Gyadi Jami’in yada labarai mai lura da kananan hukumomin shiyar Rano.